1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kamen jami'an kwastam ya bar baya da kura

Gazali Abdou Tasawa ATB(AMA
February 3, 2023

A Jamhuriyar Nijar ana ci gaba da cece-kuce kan kamen wasu tsoffin daraktocin hukumar kwastam ta kasa a bisa zarginsu da karkata wasu makudan miliyoyi.

https://p.dw.com/p/4N4iI
Shugaban Jamhuriyar Nijar Mohamed Bazoum
Shugaban Jamhuriyar Nijar Mohamed BazoumHoto: Presse- und Kommunikationsdienst der Präsidentschaft von Niger

A wannan mako hukumomin shari'ar a Nijar suka kama wasu tsoffin manyan daraktocin ma'aikatar kwastam, tare da kai su ajiya gidan yari zuwa ranar da za'a cigaba da sha'ara, wannan labari ya karade kafafen yada labarai da shafukan sada zumunta.

Rahotannin sun nunar da cewa kudade kusan miliyan dubu 20 CFA ne ake zargin sun yi batan dabo a ma'aikatar kwastam din ta kasa. Wasu bayanan na cewa jami'an kwastam sama da 100 ke da hannu a cikin wannan sabuwar almundahana da hukumar yaki da cin hanci da rashuwa "HALCIA" ta bankado a baya-bayan nan.

Karin Bayani: Badakalar kudi a bankin manoma a Nijar

A wata sanarwa da ta fitar kungiyar ma'aikatan kwastam ta kasar Nijar SNAD ta nuna rashin jin dadinta kan yadda ake kama jami'an hukumar, tare da bayyana haka a matsayin kokarin shafa wa 'ya 'yanta kashin kaji.

Sai dai kungiyoyin rajin kare hakin bani'Adama a kasar, na jinjinawa matakin, tare da bayyana cewar yana da muhimmanci shara'a ta yi wa wadanda duk ake tuhuma adalci a cikin sabon salon yaki da cin hancin da rashuwa da shugaba Mohamed Bazoum ya fito da shi na Ba-sani Ba-Sabo. Wasu na nuni da cewar akwai bukatar a fadada bincike, a yayin da wasu ke cewa akwai bukatar shugaban kasa ya sa ido domin hana katsalandan na 'yan siyasa a harkokin shari'a.

Karin Bayani: Ranar yaki da cin-hanci da rashawa a Nijar

Kungiyar ma'aikatan kwastam ta kasa ta sha alwashin gurfanar da duk wadanda suka nemi shafa mata kashin kaji a cikin wannan lamari a gaban kuliya. Kuma ta ce a shirye take ta bai wa kotu hadin kai domin gudanar da bincike kan duk wani zargi da ake yi wa membobinta.