1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Kamen wasu manyan jami'an gwamnati

Gazali Abdou Tasawa RGB
July 30, 2021

Kotu a jamhuriyar Nijar ta ingiza keyar wasu ma’aikatan gwamnati gidan maza a bisa zarginsu da hannu a badakalar almundahana da kudaden gwamnati.

https://p.dw.com/p/3yKiE
Deutschland l Besuch des Nigerianischen Präsidenten in Berlin
Hoto: Presse- und Kommunikationsdienst der Präsidentschaft von Niger

A Jamhuriyar Nijar babban mai shigar da kara na gwamnati ya ba da umurnin kargame wasu ma’aikatan gwamnati kimanin 14 da ake zargi da hannu a badakalar almundahanar kudade kimanin miliyan dubu takwas na CFA da ake zargin wani babban jami’in fadar shugaban kasa ya wawure. Tuni matakin ya soma haifar da ka ce-na ce a tsakanin bangarorin siyasar kasar inda 'yan adawa  ke korafin yadda har yanzu matakin kamen, bai shafi wasu manyan jami’an gwamnati da ake zargi da hannu a ciki.

Karin Bayani:  Nijar: Shirin yaki da cin-hanci da rashawa
 
Babban mai shigar da kara na gwamnatin Nijar, ya bayar da umarnin kargame mutanen bayan da ya kwashe sao'i yana sauraran su daya bayan daya kan badakalar da aka fi sani da badakalar  Ibou Karadje, babban ma’aikaci a fadar shugaban kasa wanda ake zargi da yin amfani da tambarin sa hannu na boge wajen karkatar da akalar kudi kimanin miliyan dubu takwas na CFA tare da hadin bakin wasu jami’an baitilmali da na ma’aikatar kudi ta kasa. Ko da shi ke cewa, hukumomin shari’ar kasar ta Nijar ba su fito fili suka bayyana adadin ma’aikatan gwamnatin da aka ingiza keyar tasu zuwa gidan maza ba, wasu jaridu masu binciken kwakwaf, sun ambato cewa mutanen sun kai akalla 14. 


Karin Bayani:  Nijar: Bincike kan karkatar da kudaden kasa

Shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum, wanda tun a lokacin hawansa mulki ya kaddamar da shirin yaki da cin hanci da rashawa da ya yi wa lakabi da ''Ba sani ba sabo'' ya bayar da umurnin gudanar da bincike kan wannan badakala ta shafi wani jami’in fadar tasa, bincike da 'yan kasa ke yi wa kallon zakaran gwajin dafin hanzari Shugaba Bazoum  Mohamed na iya yin nasara ko kuma yin raggon kaya a cikin kokowar da ya dauko ta yaki da cin hanci da rashawa a Nijar.