1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsawaita aikin rubuta sunayen masu zabe

Abdoulaye Mamane Amadou/ MNAJuly 16, 2015

A wani yunkuri na ba wa dukkan 'yan Nijar damar mallakar katin zabe gabanin zaben badi, mahukuntan kasar sun kara wa'adin aikin ba da katin zaben.

https://p.dw.com/p/1G08N
Mali Parlamentswahlen 15.12.2013
Hoto: Habibou Kouyate/AFP/Getty Images

Hukumar da ke aikin rijistar sunayen masu zabe a Jamhuriyar Nijar CEFEB ta kara wani wa'adi na kwanaki domin kara rubuta sunayen mazauna birnin Yamai a cikin sabon kundin rajistar masu zabe. Wannan dai na zama wani yunkuri na bai wa ko wane dan kasa izinin mallakar katinsa domin jefa kuri'a a zabubbukan da ke tafe a shekara ta 2016.

A yayin wani taron manema labarai da ta jagoranta dai ne hukumar ta ce ta lura da samun babban gibi a wasu biranen cikinsu har da babban birnin Yamai, inda wadanda aka tantance ba su wuce kashi 57 cikin 100 ba daga cikin kiyasin da hukumar ta yi na wadanda suka cancanci shiga kundin.

Kimanin mutum dubu 613 daga cikin mazauna birnin Yamai din da aka kiyasta sun haura miliyan daya da dubu 300 ne ta kamata a ce hukumar ta CEFEB ta tantance da kuma rubutasu a cikin sabon kundin rijistar sunayen wadanda suka cancanci zabe domin jefa kuri'unsu a zaben na 2016.

Jerin matsaloli lokacin yin rajistar zabe

Sai dai wasu matsalolin da dama da suka dabaibaiye aikin cikinsu har da rashin tarar da jama'ar a gidajensu domin tantancesu sun kawo wa hukumar ta CEFEB cikas, inda ta kasa cimma wannan gurin. Maimakon hakan hukumar ta rubuta ne kawai jama'ar da ba su wuce dubu 351 ba, abubuwan da suka nuna karara da hukumar na da babban jan aiki a gabanta.



Ban da haka ma dai sakamakon ya sha tayar da jijiyoyin wuyar jama'a da dama, cikinsu har da 'yan siyasa da kungiyoyin kare hakkin dan Adam da suka yi ta sukar lamirin aikin na hukumar wanda bai wuce kashi 57 cikin 100 ba, alhali kuwa gejin al'kalumman na zabe na bukatar samun akalla kashi 60 cikin 100 na adadin jama'ar da suka cancanci zabe da ta kamata a ce an rubuta.

Niger Niamey Opposition
Wani jarin gwanon 'yan adawa a NijarHoto: DW/M. Kanta

A yayin wata ganawa da manema labarai dai hukumar ta ce za ta zage damtse domin bai wa abinda ta kira mara da kunya.
Malam Abdourahmane Assumana kakakin hukumar ne na CEFEB.

"Za mu sake komawa gida gida tun da akwai gidajen da kamar an shiga an tarar da matar an yi rijistarta to amma mijin ba a yi rijistarsa ba, saboda baya nan. Shi kuwa wannan aikin ya ce dole sai mutum yana nan. Za mu tsaya da kanmu da mu da 'yan Yamai da sauran abokan aikinmu. Mun ma yarda aikin da cewar namu ne za su shiga domin ganin wannan matsayin na Yamai ya fice."

Da ma an san za a fuskanci matsala


Da take tsokaci a kan batun babbar jam'iyyar adawa ta MNSD Nasara cewa ta yi daman tun ran gini ake zane, saboda take-taken da ta lura, hukuma na yin aikin na rijistar sunayen masu zabe ta san da cewa ba mamaki hakan kan iya faruwa. Murtala Alhaji Mamuda kusa ne a jam'iyyar MNSD Nasara mai adawa.

"Mun san dai ba a dauki matakai kwararru ba, domin kaga kamar wadanda ke zuwa suna yawon rubuta sunayen kamata yayi kowanen su yana tare da mutane hudu. Akwai bangaren adawa da bangaren masu rinjaye da na 'yan ba ruwanmu, haka da wakilin Sarki. To matslar shi ne Sarakunan sun janye don an ce babu kudin basu, an ce za a basu jikka-jikka na CFA, su kuma a da 2009 jikka uku-uku aka basu. Su kuma sun janye saboda jikka cikin wannan yanayin da akwai wuya."

Parlamentswahlen in Burundi
Kokarin ba wa kowane dan kasa katin zabeHoto: picture-alliance/AP Photo/G. Ngingo

Tuni dai kungiyoyin fararen hular da suka ce za su kasa su tsare har ma su kiyaye su raka su dauko daga batun rubuta sunayen jama'a a cikin sabon kundin zabe har izuwa shi kanshi zaben. Sun fara nuna gamsuwa kan wannan sabon mataki na hukumar kamar yadda Alhaji Souley Oumarou na kungiyar Monsadem ya yi karin haske.

"Fata guda garemu, a yi zabe na gari, a yi zabe ba tare da wani ya fito ya ce an cuceni ko wata ta fito ta ce an cuceni ba. Hakan muke bukata."

Sai dai hukumar ta ce tana bukatar yarda da kyakkyawan hadin kai daga bangarori daban-daban na kasar, domin kammala aikin ta mai nauyi da ke a matsayin share fage ga shiga samar da wani kundin na zamani mai suna "Fichet Biométrique" da hukumar ke son samarwa.