1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cin zarafin mata ya farraka 'yan Afirka ta Kudu da Lesotho

August 16, 2022

Afirka ta Kudu ta sake fadawa cikin wata sabuwar takaddama ta kyamar baki da ake zargi da yi wa mata fyade. Hare-haren da ake kai wa 'yan ciranin ya sa suma suke mayar da martani da mai zafi.

https://p.dw.com/p/4Fb4B
Präsident Südafrika Cyril Ramaphosa
Hoto: Johanna Geron/Reuters/AP/picture alliance

Wadanda ake zargin dai na aiki ne a Ma'aikatar Hakar Ma'adinai da ke yankin Krugersdorp na Afirka ta Kudun. 'Yan kasa da zargin fyaden ya fusatasun yi yunkurin daukar doka a hannunsu, inda suka lakada wa wadanda suka yi katarin haduwa da su a wajen hakar ma'adanan duka na tozartawa a gaban jama'a.

Mata takwas fyade ne aka yi wa fyaden bayan da masu laifin suka kwace wa matan kayayyaki masu muhimmanci.

Tashin hankali da ya biyo bayan lamarin ya sanya hukumomi kama sama da mutum 100 bisa zargin su da hannu a ta'asar, kuma gaba dayansu baki ne da suka shigo Afirka ta Kudu daga Lesotho da ke makwabtaka, lamarin da ya kara tayar da daddiyar matsalar kyamar baki da kasar ta yi kaurin suna a kai.

Wasu masu zanga-zangar kyamar baki a Afirka ta Kudu a 2020
Wasu masu zanga-zangar kyamar baki a Afirka ta Kudu a 2020Hoto: Milton Maluleque/DW

Dan Afirka ta Kudu Raul Ndanduleni ya jefi baki 'yan ciranin da laifin fyaden.''Su suke fataucin mutane, su suke fashi suna kwace wa mutane motocinsu, amma da wuya a gane hakan don mahukunta ba su da cikakken bayanansu''

Wani dan fafutukar ganin an mayar da baki kasashensu Veli Madondo ya ce tun da gwamnatin Afirka ta Kudu ta gaza daukar mataki, to su za su dauki matakin nemar wa yankinsu mafita.

Yadda zanga-zangar kyamar baki a 2008 ta raunata wani mutum a Afirka ta Kudu
Yadda zanga-zangar kyamar baki a 2008 ta raunata wani mutum a Afirka ta KuduHoto: dpa

Gwamnatin Afrika ta Kudun ta amince da jan aikin da ke a gabanta a kokarin da take na ganin ta magance matsalar da baki 'yan cirani ke haifarwa a kasar. Ministan harkokin cikin gida Aaron Motsoaledi ya ce ''a duk lokacin da muka dauko batun daukar mataki kan bakin da suka hana ruwa gudu sai ka ji an ce, Afirka ta Kudu na kyamar baki amma ko kadan ba haka bane, matsala ce babba da ke bukatar daukar sahihin mataki kuma yin hakan na bukatar hadin kan al'ummar Afirka ta Kudu baki daya'' in ji ministan.

Mutane da dama sun mutu tun bayan soma rikicin nuna kyama ga baki a shekarar 2008.