1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mahimmancin dokoki lokacin zaben Nijar

Abdoulaye Mamman Amadou/PAWOctober 8, 2015

Masana sun ce jahiltar shika-shikan ka'idojin siyasar kasa na iya haifar da yawan rudani da ma tashe-tashen hankula a lokutan zaben da ake shirin gudanarwa a farkon shekara mai zuwa na 2016.

https://p.dw.com/p/1Gkj6
Niger Wahlhelfer in einem Wahllokal in Tahoua
Hoto: DW

A jamhuriyar Nijar wasu masana dokokin kasar ne da masu fashin bakin siyasa suka nuna fargabarsu kan abin da zai iya faruwa a yayin zabubukan da ke tafe a kasar, sakamakon tsananin jahiltar kundin tsarin jam'iyyun siyasa « Charte des Partis Politiques » da kundin zabe daga akasarin magoya bayan jam'iyyun siyasa har ma da wasu shuwagabannin jam'iyyun siyasar kasar.

"...Mutane da sunan jam'iyyun siyasa ne suke tashin hankali, to jam'iyyun siyasar nan daga yau kamata yayi su ba magoya bayansu tarbiya ta kirki..."


Dr Maina Karty Bukar ke nan, wani mai sharhi a kan dokoki kuma kwararre a fannin kundin tsarin mulkin Nijar ke bayyana fargabarsa kan abin da ka iya faruwa a zabubukan dake zuwa, muddin bakin jahilci da yin ko oho da dokokin tsarin siyasa da na zabe suka ci gaba da mamaye zukata da hankulan magoya bayan jam'iyyun siyasar Nijar, yanzu hakan dai fage da ma dandalin siyasar Nijar na cigaba da daukar wani sabon salo na bayyanar wasu kalamun batanci har ma da na zage-zage a tsakanin magoya bayan jam'iyyun siyasa. ko kuwa wani bi a tsakanin manyan shuwagabannin jam'iyyun siyasar, abubuwan da masharhanta ke yi wa kallon wani sabo kuma bakon lamurra da ka iya dagula tafarkin dimokiradiyar kasar. Dr Maina Karty kwarare ta fannin kundin tsrin mulkin nijer lokaci yayi da ta kamata a ce huntuwa ta canza zane:

"Su manyan jam'iyyun siyasar nan sun san wadannan kundayen amma su magoya bayan jam'iyyun nan ba su san wadannan kundayen ba, to jam'iyyun nan su dauki aiki, musamman ma wannan kundin na tsarin jam'iyyun siyasa su sanar da su domin idan an sansu za'a yi zabe a cikin kwanciyar hankali da wasu ayoyi na cikin kundin zabe to amma idan ba'a san da su ba za'ayi zabe a cikin tashin hankali"

Wähler vor Wahllokal in Tahoua Niger NO FLASH
Hoto: DW

"Idan bera na da sata daddawa ma na da wari" in ji 'yan adawa
A na shi bangaren kakakin jam'iyyar MNSD mai adawa Murtala Alhaji Mamuda cewa ya yi tabbas da akwai rashin samun cikakken horo, dauko daga manyan 'yan siyasar har ma i zuwa ga magoya bayan jam'iyyun na siyasa, to amma sai dai idan bera da sata to ita ma daddawa na da wari.


Niger Wahlen Politik Stimmen Auszählung
Hoto: DW/M. Kanta

"Wannan rashin horon mun san da akwai shi tabbas to amma kamar yanda na fada ne da cewar akwai kudin da gwamnati ke bayarwa da ta kasa bayarwa kuma abin duk shekara ne, ga shi yanzu har shekarar ta kusa karewa kuma tallafin na gwamnati ba ta bayar ba gaskiya a matsayi na na dan siyasa kuma musulmi wadannan ba hujja ba ce ka tunkari dan uwanka na siyasa da zage-zage abin da ake so shi ne hujjoji, mutun idan ya zo ka bashi hujja mutane su za su fadi idan har hujjar da ta ka bada ta gamsar ko a'a, idan karya ce kuma kake an sani amma bai kamata ba gaskiya a fagen siyasa a dinga zage-zage."

Talakawa sun ce kansu na hade

Kalaman batsa da zage-zage a fagen siyasa dai da ke cigaba da yawaita a yanzu na a matsayin wata sabuwar al'ada ko da yake wasu kungiyoyin fararen hulla masu fafatukar kare hakkin talakawa ire-iren su Muryar Talaka, kokawa suka yi da rashin dauriyar da wani bi 'yan siyasar kasar ke nunawa,to amma sai dai duk da hakan kungiyoyin sun ce talakawan Nijar kansu a hade, kuma ba wani dan siyasar da zai iya hadasa masu rarrabuwar kawuna domin cimma wani gurinsu irin na siyasa.

Wähler im Wahllokal in Tahoua Niger
Hoto: DW

"Ba ruwan talaka, talaka zabawa ne shi ke wanda shi ke ganin alamun adalci a gabanshi shi dauka duka su je su yi kumbala idan suna so tunda an san siyasa wurin neman abinci ne amma su daina zaage-zagen junansu suna wulakantar da kansu suna nuna mana su ba su san abin da suke a siyasa ba yanzu idan ka dubi abinda aka yi a majalisar dokokin kasar nan a shekarun baya bayan nan ai abin kunya ne sai an kai ma Nijar kana son ka zama dan mjalisaar dokoki amma ka rinka jin kunyar mutane"


A yanzu hakan dai fagen na siyasar ta Nijar na mamaye da kalamun da ma rubuce-rubuce a jaridu da alluna, kuma an wallafa wasu hutunan da ke tozarta walau shuwagabannin dake mulkin kasar ko adawa abubuwan da ake hasashe ba zai haifarma Nijar dada mai ido ba ganin irin yanda wutar fitinar ta siyasa ke kara kamari a tsakanin bangarorin adawa da na masu rinjaye.