1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kalamun kabilanci a yakin neman zaben Nijar

Salissou Boukari AMA
February 12, 2021

A Jamhuriyar Nijar kungiyoyin kare dimukuradiyya sun yi Allah wadai da furta kalaman kabilanci da bangaranci a cikin yanayin da ake na yakin neman zaben shugaban kasa zagaye na biyu.

https://p.dw.com/p/3pHlg
Niger Wahlen
Magoya bayan jam'iyyar LUMANA Afrika na gangamin yakin neman zabeHoto: picture-alliance/dpa/EPA/A. Gillis

Gamayyar kungiyoyin fararan hulla masu fafutikar kare dimukuradiyya na "Convergence Citoyenne pour la Democratie et la Republique" sun yi wannan fitowa ne na farko inda suka yaba yadda zabukan kasar suka gudana, da yabo ga hukumar zabe da ma kotun tsarin mulki ta kasar Nijar, kan yadda ta bayar da sakamakon zabe da suka ce ya dace da yadda hukumar zabe ta bayar ganin cewa kura-kuran da aka samu a zaben bai taka kara ya karya ba.

Karin Bayani: Rikicin siyasa a Nijar na neman wajen zama 

Kungiyoyin sun yi tsokaci ne domin wasu tsawatawa kan wasu tarin abubuwa da suka gano sun wakana a yayin manyan zabukan da aka gudanar na shugaban kasa zagayen farko da na 'yan majalisun dokoki. Inoussa Samna, daya daga cikin yan kungiyoyin fararan hullan ya ce "sun gamsu da yadda hukumomin biyu suka tafiyar da aiyukansu na zaben da suka gabata, sun kuma yi alfahari da 'yan Nijar kan yadda suka bi zabukan sau da kafa, ba tare da yin tashe-tashen hankula ba kamar yadda aka yi fargaba a baya."

Karin Bayani: Wacce alkibla siyasar Nijar ta dosa?

Sai dai wasu na kallon wannan fitowa a matsayin wani yunkuri na kare gwamnati da kuma dan takara na bangaren gwamnati, duk da cewa 'yan kungiyar sun ce suna yi ne da sunan yan kasa baki daya, ko da ya ke a share daya, kungiyoyin sun soki sanarwar da wata gamayyar ma’ilamtan Nijar suka fitar kan cewa a yanzu yana da kyau 'yan Nijar su yi nazari wajen zabe, kar ba su yi zaben tumun dare.