1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siyasar Nijar cikin halin ni tasku

Lateefa Mustapha Ja'afar
February 11, 2021

A karon farko rikici na neman yi wa siyasar Nijar katutu, bayan da ake ta samun kace-nace tsakanin magoya baya, tun daga lokacin yakin neman zabe.

https://p.dw.com/p/3pEjq
Wahlen Niger Niamey
Al'ummar Jamhuriyar Nijar, na shirin zuwa zagaye na byiu na zaben shugaban kasaHoto: Issouf SANOGO/AFP

Tuni dai kungiyoyin fararen hula da ke fafutukar kare dimukuradiyya a Jamhuriyar ta Nijar, suka fara fitowa fili suna yin tir da yadda wasu al'ummar kasar da ma 'yan siyasa ke furta kalaman da ke da nasaba da kabilanci da bangaranci.

Yakin neman zaben da ke tattare da rikici da kasar ta samu kanta a ciki  dai, na neman saka siyasar Jamhuriyar ta Nijar cikin halin rashin tabbas. A halin yanzu dai 'yan takarar neman shugabancin kasar da masu mara musu baya, na ci gaba da furta kalamai iri-iri a gaban dumbun magoya bayansu, inda a wasu lokutan su kan zarme su furta kalaman da ba su dace ba.