1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kada gangar siyasa a Nijar

Gazali Abdou Tasawa AH
February 8, 2021

A Jamhuriyar Nijar, dan takarar gwamnatin Bazoum Mohamed da na adawa Alhaji Mahamane Ousmane sun kaddamar da yakin neman zabe dukkanin su a Tillabery a zagaye na biyu na zaben shugaban kasa da ake shirin yi.

https://p.dw.com/p/3p4M5
Niger Wahlkampf - Mohamed Bazoum
Hoto: Getty Images/AFP/B. Hama

Da farko dan takarar adawa ne Mahamane Ousmane ya kaddama da yakin neman zaben a Jihar Tillabery da ke a yammacin Njar. A jawabin da ya gabatar a wajen wannan taro dan takarar adawa Alhaji Mahaman Ousmane ya bayyana daurin kansa a game da yadda matsalar tsaro ke kara kamari a Nijar tare da shan alwashin kawo karshen wannan matsala idan an zabe shi.

Dan takarar adawa Mahamane Ousmane ya kaddamar da kampe din sa shi ma a Tillabery

Plakat Ousmane
Hoto: DW/M. Kanta

Yayin da a yau kuma dan takarar jam'iyyar da ke mulki ta PNDS taraya Bazoum Mohamed ya kaddamar da yakin neman zabensa a Jihar ta Tillabery. Madugun ‘yan adawqar Nijar Malam Hama Amdou wanda ke da karfin fada a ji a cikin Jihar ta Tillabery ya yi kira ga al’ummar yankin da ta yi watsi da duk wata akida ta kabilanci ko bangaranci da wasu ‘yan siyasa ke yadawa domin kishin kasar nan ta hanyar jefa wa Mahaman Ousmane kuri’a. a zaben mai zuwa