1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

CSC ta gana da 'yan siyasa a Nijar, gabnin zabe

Gazali Abdou Tasawa
October 27, 2020

A Jamhuriyar Nijar Hukumar Sadarwa ta kasar wato CSC ta gana da wakilan 'yan siyasar kasar, inda bayyana musu sababbin ka'idoji da ta samar domin ganin an tabbatar da adalci ga jam'iyyun siyasa a kafafen yada labarai.

https://p.dw.com/p/3kUuh
Niger Staatliches TV und Radio in Niamey
Gidan talabijin da radiyo na ORTN, mallakar gwamnatin Jamhuriyar NijarHoto: DW/M. Kanta

Hukumar ta CSC mai kula da kafafen yada labaran karkashin jagorancin shugabanta Dokta Kabir Sani dai, ta tattara wakillan jam'iyyun siyasa da na sauran 'yan takara a zabukan kasar da ke tafe domin gabatar masu da jerin dokoki guda takwas, wadanda ke kunshe da ka'idojin da 'yan siyasar ya kamata su cika da kuma sharuddan da ya kamata su kiyaye a sakonninsu na yakin neman zabe da za su gabatar, a kafafen yada labarai na gwamnati da ma masu zaman kansu. 

Karin Bayani: Nijar: Masana dokoki na fuskantar barazana

Sai dai da yake tsokaci a game da wannan shiri na hukumar ta CSC, Honorable Issaka Manzo wakilin jam'iyyar RDR Canji guda daga cikin jam'iyyun adawar kasar, ya nuna shakkunsa dangane da mutunta tsarin da hukumar ta CSC ta gabatar musu, musamman a kafafen yada labarai na gwamnati.

Niger DW Hörer
CSC ta shimfida ka'idojin yakin neman zabe a kafafen yada labarai ga jam'iyyu a NijarHoto: DW/A. M. Amadou

Amma a nasa bangaren Shugaban Hukumar Sadarwar, ya sha alwashin ganin kaucewa duk wasu kura-kurai da aka fuskanta a baya da suka haifar da korafe-korafen 'yan siyasa musamman ma bangaren adawa.

 Karin Bayani: Rawar da sojoji suka taka a siyayar Jamhuriyar Nijar

Sai dai a daidai loakcin da 'yan adawar ke nuna shakkunsu game da aiwatar da wannan tsari na yin adalci wajen ba da damar amfani da kafafen yada labarai a lokacin yakin neman zabe, Malam Adamou Mouhamadou na jam'iyyar Jamhuriya ta bangaren masu mulki, bayyana gamsuwarsa ya yi a kan shirin, tare da yin fatan ganin 'yan siyasar na kowane bangare sun kiyaye doka. Tsarin da hukumar ta CSC ta gabatar ya kuma tanadi bai wa 'yan siyasar damar gabatar da sakonnin yakin neman zabensu a kafafen yada labarai masu zaman kansu, amma a cikin wani lokaci takaitacce, tare kuma da kiyaye furta duk wasu kalamai da ka iya haifar da hatsaniya.