1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakatar da amfani da ajujuwan zana a makarantun yara a Nijar

Gazali Abdou Tasawa MNA
November 19, 2021

Hukumomi a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar za su fara aiwatar da matakin hana amfani da ajujuwan zana a makarantun kananan yara bayan gobarar da ta halaka kananan yara 26 a wata makarantar kananan yara a garin Maradi.

https://p.dw.com/p/43GmR
Niger | Brand einer Schule in Niamey
Hoto: Marou Madougou Issa

Gwamnan birnin na Yamai Malam Oudou Ambouka ya kira taro na masu ruwa da tsaki kan harkokin ilimi domin yin bitar adadin ajujuwan zanan da ke da akwai a cikin birnin, musamman a makarantun kananan yara, da kuma daukar matakan gaggawa na samar da sabbin ingantattun ajujuwa ga kananan yaran da aka cire daga na zana a bisa umurnin gwamnatin Nijar kamar dai yadda gwamnan ya bayyana a lokacin bude zaman taron.

"Tun bayan iftila'in da ya wakana a Jihar Maradi, gwamnati ta dauki matakin dakatar da amfani da ajujuwan zana a makarantun kananan yara a kasa baki daya. Wannan mataki ne mai muhimmanci, kuma umurni ne mai karfi da aka ba mu, da ya zama dole mu yi biyayya gare shi."

Karin bayani: Nijar: Gobara ta halaka dalibai a makaranta

Binciken farko dai ya nunar da cewa akwai ajujuwan zana kusan 400 a fadin birnin daga ciki kimanin 60 na kananan yara. Malam Ibrahim Nalado mataimakin shugaban kungiyar iyayen yara 'yan makaranta ta kasa baki daya, daya daga cikin mahalarta taron da gwamnan ya kira, ya yi karin bayani kan matakan gaggawa da taron ya dauka na tunkarar wannan matsala da ta shafi kananan yaran 'yan makarantun reno.

"Ajujuwa 60 ake bukata cikin gaggawa, idan ba a samu ba, dole yaran za su koma gida. Ba ma son yaran su koma gida tun da ba mafita ba ce."

A kauyen Tibiri da ke kusa da Maradi akwai ginin zamani na makarantar yara da wata kungiya mai zaman kanta ta kasar Luxemburg ta gina
A kauyen Tibiri da ke kusa da Maradi akwai ginin zamani na makarantar yara da wata kungiya mai zaman kanta ta kasar Luxemburg ta ginaHoto: picture alliance / ZB

Bangarori da dama ne dai da suka hada da makarantu masu zaman kansu na cikin birnin na Yamai suka fara bayar da tasu gudunmawa ta samar da ajujuwan ga kananan yaran a cikin gaggawa domin ba su damar ci gaba da karatunsu.

Karin bayani: Nijar: An yi Jana'izar dalibai 27 da suka rasu a gobara

Mahukuntan birnin na Yamai sun kuma yi kira ga kamfanonin salula da bankuna da sauran masu hannu da shuni da su kawo tasu gudunmawa ta ganin an samar da ingantattun ajujuwan da ake bukata domin maye na zana da ke da akwai a illahirin makarantun birnin nan da 'yan shekaru.

Wasu alkalumman kididdiga sun nunar da cewa akwai ajujuwan zana kimanin dubu 36 a fadin Nijar. Kuma

dan kudin gina ingantaccen aji daya na tashi miliyan bakwai na CFA kamar yadda kwararru suka nunar, to kuwa gwamnatin Nijar na bukatar kudi tsaba miliyan dubu 250 na CFA domin maye gurbin illahirin ajujuwan zana na kasar da ginannun ajujuwa.