1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojojin Najeriya sun yi bore a Maiduguri

August 13, 2018

An shiga rudani a Maiduguri lokacin da Sojoji kimanin 300 suka yi tawaye a filin jirgin sama, bayan da aka nemi sauya musu wurin aiki zuwa kan iyaka da Nijar.

https://p.dw.com/p/334l2
Symbolbild Nigeria Armee
Hoto: picture alliance/AP Photo/Gambrell

Sojojin wadanda suka fusata sun ki shiga jiragen sama da aka shirya kwashe su zuwa sabon wurin aikin su da ke karamar hukumar Marte a jihar Borno, inda su ka yi ta yin harbi a sama. Sojojin sun kuma yi barazana ga man'yan jami'an su da suka nemi rarrashin su domin zuwa sabon wajen aiki.

Nigeria Soldaten Boko Haram ARCHIVBILD
Dakarun Najeriya yayin wani atisayen kasa da kasaHoto: Reuters

A cewar Sojojin, sama da shekaru hudu suna yaki da Boko Haram a Borno ba tare da an maida su wuraren su na asali ba, abinda su ka ce ya saba da yanayin aikin Sojoji. Daya daga cikin Sojojin da ya bukacin DW ta sakaya sunansa, ya bayyana cewa: "Mun hau Bom, an harbe mu an mana kwanton bauna, duk muna nan tsawon shekaru hudun nan. Bama samun lokacin iyalanmu tsanani a baka kwana 14 ka je ka ga iyalanka, Saboda haka mun yi kokarinmu a kawo wasu. Shi ya sa muke zanga-zanga saboda Janar Buratai ko Shugaba Buhari su ji halin da muke ciki”

Nigeria Soldaten an einem Checkpoint in Gwoza
Wata mata a shingen binciken Sojoji a GwozaHoto: picture-alliance/AP Photo/L. Oyekanmi

Sani Umar wani mai sharhi kan harkokin tsaro, ya ce: "Yanayin na da hadari, ya kamata mahukunta su gaggauta daukar mataki."

Lamarin ya jefa jama'ar gari cikin fargaba, amma rundunar Sojin Najeriyar ta ce kura ta lafa kuma wasu tsirarun Sojoji ne ke neman turje wa sauyin wurin aiki, wanda kuma ba bakon abu bane. Boren Sojojin na zuwa ne bayan da wasu ‘yan sanda suka yi bore a Maiduguri saboda rashin biyan su hakkokinsu.