1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar ta yi asarar sojoji mafi girma a Inates

Abdourahamane Hassane
December 19, 2019

Sojoji kusan 71 Jamhuriyar Nijar ta rasa a wani harin ta'addanci da kungiyar IS ta kai a sansanin sojojin Inates da ke a yammacin kasar kan iyaka da Mali daf da bikin ranar jamhuriya na cikon shekaru 61.

https://p.dw.com/p/3V586
Niger Armee | Opfer nach Angriff
Hoto: DW/S. Boukari

Wannan shi ne irinsa hari na farko mafi muni da rundunar sojojin Nijar din ta fuskanta a cikin sama da shekaru goma, wanda ta rasa sojoji 71 a sakamakon hare-haren da kungiyar IS ta kai a sansanin sojojin Inates da ke a yammacin kasar kan iyaka da mali. Yanzu haka wannan hari ya janyo muhawara a sahun al'umma da ke zargin sojojin Faransa da mara wa 'yan ta'addar baya.